Ku yi Watsi da Tsarin Mulkin 1999, ku rungumi na 1960 muddin ana son gyara ƙasa – In Ji Akande

FB IMG 1705308257452

“Ku yi Watsi da Tsarin Mulkin 1999, ku rungumi na 1960 muddin ana son gyara ƙasa” Akande ya fadawa NASS

Alfijir labarai ta rawaito tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Cif Bisi Akande ya bukaci ‘yan Majalisarsar Tarayya da su amince da kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1960 domin ci gaban ƙasar.

Akande ya shawarci ‘yan Majalisar tarayya da su yi watsi da kundin tsarin mulkin 1999 da shugabannin sojoji suka rubuta domin kasar ta yi aiki da shi.

Tsohon Gwamnan Jihar Osun ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a ranar Asabar gabanin bikin cikar ranar haihuwar sa, shekaru 85 a duniya.

Jigon na Jam’iyyar APC ya ce sake farfaɗo da martabar kasar ba ya bukatar wani abu da ya wuce yin watsi da kundin tsarin mulkin ƙasarsar na 1999.

Ya ce kundin tsarin mulkin 1999 ba wani ne ya rubuta shi ba, don haka dole ne Majalisar Dokoki ta ƙasa ta koma kan tsarin mulkin kasar na ainafi.

Akande ya ce “na fi gamsuwa da kundin tsarin mulkin 1960 ga Najeriya, shi ne ya fi kyau. misali, a kundin tsarin mulkin 1960 idan kai dan Majalisar wakilai ne na kasa da na Jiha, to aikin ka ya kasance na ɗan lokaci ne, wato zai baka damar cigaba da aiki da kake yi, domin siyasa ba ta aiki ba ce a lokacin.

Ya koka da cewa sojoji sun sauya salon yadda ake shigar da kuɗaɗe da kuma kashe kuɗaɗe masu yawa a cikin harkokin siyasa waɗanda ba su taimaka wa kasar.

Saboda ƴan Siyasa na son ci gaba da mulki na dindindin sai suka fara amfani da kudi wajen biyan Sojoji albashi mai tsoka, don haka kowa ya bar aikinsa ya zama dan siyasa,” inji shi.

Ka bar aikinka da kake yi duk saboda Siyasa, ka zama dan siyasa, ba abin da za ka iya samarwa, sannan kana son zama mai tarin dukiya, Kenan ka zama na karya, domin kuwa ka ka rabu ne da kyawawan akan abu mara kyau.

Ya yi gargadin cewa “Har sai kun koma ga salon baya sannan za a iya samun cigaba, idan kuna maganar sake fasalin ƙasar ne to ku jefar da wannan kundin tsarin mulki na yanzu wanda ba wani ne ya rubuta shi ba, sannan ku rungumi tsarin mulkin 1960, sai kuyi la’akar da hakikanin halin da ake ciki a yau domin dai-daita shi”.

News NG

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *