Kudirin Gyaran Dokar Masarautun Kano ya Tsallake Karatun Farko

FB IMG 1716413044880

Majalisar dokokin jahar kano ta gudanar da karatu na daya akan kudirin gyaran dokar kafa masarautun kano a karo na biyu wacce shugaban masu rinjaye kuma wakilin karamar hukumar Dala Alh. Lawan Hussaini Chediyar ‘Yan Gurasa ya bijiro da ita.

Alfijir labarai t rawaito Akawun majalisar Alh. Bashir Idris Diso ne ya gabatar da karatu na dayan bayan da shugaban masu rinjayen ya karanto kudirin.

Majalisar ta bukaci gwamnatin jahar kano ta gina titin daya tashi daga makarantar mata ta Jogana zuwa Kadewa zuwa Baburko Yafata zuwa garin Nahuche Andawa dake garin Gezawa.

Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Gezawa Abdullaji Yahaya Tsamiyar Kara shi ne ya gabatar da kudirin a zaman majalisar na yau da manufar saukakawa al’umar yankin gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Har ila yau majalisar ta bukaci gwamnatin jahar kano ta gina hanyar da ta shi daga Kwanar Freedom zuwa Tarauni zuwa Jigoro a karamar hukumar Gezawa.

Bukatar hakan ta biyu bayan kudirin da dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Gabasawa Alh. Zakariyya Abdullahi Nuhu ya gabatar inda ya ce al’umar yankin suna fuskantar wahala saboda lalacewar hanyar.

Shugaban majalisar Alh. Jibril Isma’il Falgore ne ya jagoranci zaman majalisar na ranar Larabar nan.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *