Kun San Mecece Duniyar Mafarki METERVERSE kuwa?

 METAVERSE SABUWAR DUNIYAR MAFARKI INTERNET.

Best Seller Channel


Sadeeq Dantsoho Sipikin 

Gabari


Best Seller Channel 

Idan ba zaku manta ba a cikin watan October na shekar 2021 shugaban Kamfanin Facebook ya bada sanarwa cewa ya maye sunan kamfaninsa da META. wannan dalilin ya jawo cheche kuche game da ko wanne daliline ya jawo haka ko me hakan take nufi?

Saboda sanin muhimmanchin kafofin sadarwa na dandalin sada zumumchi yasa nake tambayar kaina wai mene METAVERSE (META) dinnan.

Ita dai wannan kalmar da ta dauki hankali kuma zata chigaba da zama abun tattaunawar da zaayi ta magana akansa nan da zuwa shekaru ashirin masu zuwa. 

METAVERSE wani mafarki ne da akeyi akan cigaban yanar gizo kuma ake kashe makudan kudade domin aiwatar da bincike da gwaji don ganin wannan mafarkin ko duniyar ta tabbata.

Best Seller Channel 

Kalmar Metaverse dai ta samo asali daga wani littafin da aka wallafa  mai suna (Snowcash) a chikin shekarar 1992, mallakar Neal stephson.

Metavese sabuwar duniya ce ta ayyanawa (Imagination) da kuma tafiyar zuciya da hankali akan internet, ita wannan Kafa zata canza sadarwa daga rubutu da sako zuwa ido na ganin ido ko kuma ga fili ga Mai doki.

Ta yadda zai iya yi yuwa ka zauna kayi gani da wanda yake Japan ko America kamar kuna zaune Kai dashi akan benci daya a guri daya.

METAVERSE DUNIYAR MAFARKI

Ta yadda zaka shiga meeting kamar yadda yanzu ake zoom da goggle meet ta hanyar video da audio, to shi META zaizo da Yanayin da zaka kasance da wadanda kuke meeting a guri daya kuna ganin juna (imaginary) kuma kuna exchanging ideas  kamar duk a zaune kuke a cikin daki daya ta hanyar META world.

Metaverse zai zamo wata duniya da zaka sayi Fili (plot) ka gina shago, ka kwawata shi kuma kurwarka ta zauna a ciki ta gudanar da rayuwa kamar yadda ake gudanar da rayuwa a gaske.

Best Seller Channel 

Za’ayi wasanni, kasuwanci, al amuran rayuwa, karance-karance da duk wani more rayuwa da ka Sani ta hanyar imagination.

Ya za’ayi hakan ta kasance?

Sanin kanku ne yanzu idan aka tashi kakanninmu akace musu ana video call, instant messaging da zoom meet ba zasu yarda ba, to kamar haka META World zata kasance.

Shi dai Marck Zuxkerberg tuni ya ware wasu zunzuritun kudade domin yin bincike yadda social Media ta Facebook zata koma wani abu kamar META world.

1) Za’a kera AR Glasses.

2) Wrist Band

3)VR Headset domin tabbatar da samuwar Meta world.

Kamar yadda muke ganin virtual games da ake hawa wani abu Mai kamar lilo sannan a saka AR Glasses sai mutum ya ganshi cikin daji yana ta tsallake tsallake, wani lokaci har ihu zaka ga wasu sunayi saboda imaginary feelings of Virtual reality, to tsarin Metaworld zai zamo kamar haka zaka saka AR Glasses kayi attending event a virtual world ko kayi meeting da mutanen America, Japan, ko kuyi Game kamar kuna tare.

Best Seller Channel 

Ranar 10 Ga watan Disamba na shekarar 2021 Wani sanannan Attajiri Bill Gate yayi wata tattaunawa da Jaridar Business insider ta America. 

Yana bayyana Cewa nan da shekara uku duk wasu taro da akeyi a duniya ta hanyar virtual presentation zai koma Meterverse. 

Bill Gate ya Kara da cewa duk wani Videos meeting zai koma ta hanyar mutum ya kirkiri kurwarsa wato (Avartar) a cikin duniyar Meta domin mu’amalar yau da kullum.

METAVERSE DUNIYAR MAFARKI

Jaridar Yanar Gizo ta PCmag.com to 16 ga watan Nuwamna 2021 ta ruwaito Mack  Zuckerber Attajiri mai kamfanin FACEBOOK ya fitar da wata Safar hannu mai dauke da sensor wacce za’ayi amfani da ita wajen taba wasu abubuwa a cikin duniyar META wannan yana zuwa bayan Binciken don kirkirar agogo da Kuma tabarau da za’ayi domin shiga duniyar METAVERSE.

Shi dai wannan tsari na Metaverse shine mafi kololuwar Fasahar kimiya da wayewar da bil’adama yake kokarin samarwa Kuma yana nan tafe ko kusa ko nesa.

Sannan duk wani tsarin biyan kudi da za’ayi a METAVERSE world of virtual reality za’a biyane da kudin Crypto Currency, ita kanta Fasahar Meterverse zata samu ne daga Blockchain technology. 

Wannan Fasahar ta Meterverse zata iya Samar da dawwamammiyar kasuwa ta Cinikin Cryptocurrency idan har ta samu gurin Zama.

Tun-tuni kamfanunuwa da irinsu Decentraland (MANA) KOLLECTIBLES (KOL) SAND suka fara siyar da fulotai da Estate da manyan shaguna a cikin duniyar METERVERSE.

Kamfanunuwa da dama sunyi nisa wajen siyan sarari a cikin duniyar meta da kuma yin bincike domin bunkasa ta.

Best Seller Channel 

Masanan sun bayyana Cewa Kamar yadda muke bata lokaci akan yanar Gizo haka ake tunanin mafi akasarin rayuwarmu sai mun fi gudanar da ita a Metaworld fiye da reality world.

Allah shine masani.

Naku

 Sadeeq Dantsoho Sipikin Gabari.

Zaku iya samuna a sadeeqsipikin@yahoo.com

Slide Up
x