Kungiyar Ƙwadago ta Bayyana Ranar da Zata Shiga Yajin Aiki a Najeriya

Screenshot 20231103 172349 com.android.chrome edit 94247829761139

Manyan kungiyoyin kwadagon biyu sun ce sun fara hada Kan mambobinsu a fadin kasar nan ba tare da bata lokaci ba .

Alfijir Labarai ta rawaito Shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC sun sanar da shiga yajin aikin gama gari a fadin kasar daga ranar Talata 14 ga watan Nuwamba 2023.

Shugabannin kungiyoyin biyu sun cimma wannan matsaya ne bayan wani taron majalisar zartarwar su ta kasa na musamman da aka yi ranar Talata a Abuja

Manyan kungiyoyin kwadagon biyu sun ce sun fara hada Kan mambobinsu a fadin kasar nan ba tare da bata lokaci ba .

Matakin da kungiyar kwadagon ta dauka ya biyo bayan cin zarafin shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero da jami’an tsaro suka yi a makon jiya a jihar Imo.

An dai yi ta cece-ku-ce daga kungiyar kwadagon da ke zargin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Imo, Mohammed Barde da hannu a harin da aka kai Ajaero a Owerri, babban birnin jihar Imo.

Kungiyar Kwadago a ranar Juma’ar da ta gabata ta baiwa Gwamnatin wa’adin kwanaki biyar domin ta maye gurbin kwamishinan ‘yan sandan, yayin da ta kuma zargi Gwamna Hope Uzodimma da ke neman a sake zabensa da harin da aka kai wa Ajaero duk da cewa Gwamnan ya ce ba shi da hannu a harin da aka kai wa shugaban kwadagon.

Kungiyar Kwadago ta kuma bukaci a kama tare da gurfanar da wasu daga cikin hadiman gwamnan tare da yin barazanar ɗaukar matakin yajin aiki a fadin Nigeria idan ba a aiwatar da bukatun nasu ba.

Tuni dai, Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, a ranar Lahadi, ya sauyawa Barde wajen aiki sakamakon karatowar zaben gwamnan jihar Imo da za a yi a ranar 11 ga Nuwamba, 2023.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *