Kungiyar Masu Daukar Hoto Ta Jihar Kano Ta Zabi Sabbin Shugabaninta

IMG 20240701 WA0178

Hadaddiyar Kungiyar masu sana ar daukar hoto ta jihar kano ta gudanar da taro a jiya 30/6/2024 a harabar garden dake karkashin Gawar Dangi.

Taron ya samu halartar mayan shuwagabannin kungiya Kamar su chairman da secretary da ma ajin kungiya da dai sauran manyan masu hotuna.

Alhamdulillah antattauna sosai akan yadda kungiya zata cigaba da kuma kawo sauyi a cikin ta, in da chairman Alhaji Ado Aps ya bayyana yadda wannan kungiya ta samo asali da lokacin da aka kafata har kawo yau, wanda shi yake jagorantarta tun daga 2012 zuwa yau.

Shugaban ya bayyana saukarsu daga kan mukamansu domin a sake sabon zabe domin kawo ci gaba cikin sana ar, in da  aka nada sababbin shugabanin riko.

A yayin wannan zaman  gida ya amince da nadin Dr sani maikatanga a matsayi shugaba da kuma Nasir Rabiu tubles a matsayi mataimaki sai Balancy mai magana da yawun kungiya.

Taron an yi shi lafiya cikin kwanciyar hankali da annashuwa tare da goyon kowa bayan kowa akan hakan.

  Daga karshe shugaban riko yayin nasa jawabin nasa yayi Alkawarin kawo canji da kuma dorawa akan tsarin da tsofaffin shuwagabannin suka yi na jajirce sosai don kawo cigaba a kano da Nigeria baki daya.

Adress din kungiya No 45 Lawan Danbazau Road Balancy Photography

Muna godiya sosai Allah ya taimaki jihar kano da Nigeria gaba daya ya sawa sanarmu albarka ameen

Sa Hannu (Dr)  Balarabe u Abdullah FIPPS Balancy Africa PRO

Screenshot 20240701 135249 Samsung Notes
Balancy

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *