Wannan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabar kungiyar kwamrade Aisha Muhammad Yalleman da kuma sa hannun sakataren kungiyar Kwamrade Muzamil Ibrahim Yakasai.
Alfijir labarai ta rawaito cikin sanarwa, Kwamrade Aisha ta ce, Kwamrade Ladan ta cancanci matsayin da ta samu na sakatariya, sakamakon kwazonta da hangen nisanta akan ‘yan Jaridu mata a fadin Najeriya.
Sanarwa ta kuma ta ya Hajiya Aisha Ibrahim Bura murna a matsayin sabuwar shugabar kungiyar NAWOJ.
Kwamrade Aisha Yalleman ta yi fatan Hajiya Bura za ta hada kan ‘yan jarida mata na kasar nan, da nufin ciyar da kungiyar gaba, tare da fatan cewa, kungiyar za ta ci gaba da bai wa ‘yan jaridun horo akai akai ganin yadda aikin jarida a yanzu ke tafiya da zamani.
An dai gudanar da zaben kungiyar ta NAWOJ a ranar Asabar, Ashirin da biyar ga watan Nuwanban nan da muke ciki, a birnin tarraya Abuja.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp