Kwamandan Hukumar Yaki da ‘Yan Ta’adda Bello Bakyasuwa ya Tsallake Rijiya da Baya

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Alfijr ta rawaito Kwamandar hukumar yaki da yan ta,adda Bello Bakyasuwa ya tsallake rijiya da baya a kan hanyarsa daga Gusau zuwa kaduna, a lokaci da wasu da besan ko su wayeba suka tare shi a Kan hanya a lokacin da zai bar gari.

Hakan yana kunshe ne cikin wata takarda Mai dauke da sa hannunsa wadda ya rabata ga manema labarai a garin Gusau, ya Kara da cewa a halin yanzu yana kwance a gadon asibiti, ya ce rayuwanshi na cikin hadari, in da ya Kara da cewa yana fuskantar barazana a koda wani lokaci.

Bakyasuwa yace yadda abin ya faru shine, kwanaki hudu da suka wuce a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Funtua-Zaria, sai ya lura cewa motoci biyu kirar Hilux da BMW suna bina a baya, sai ya tsaya a Yankara suka wuce shi.

Ya ce“Mutanen da ke cikin motocin biyu ne suka fara harbin motar da nake ciki, bayan na ci gaba da tafiya kuma na samesu a hanya, mun kwashe ‘yan mintuna muna musayar wuta da su sai da na tsere na gudu cikin daji duk jikina jini.

Sai dai daga bisani bayan kamar mintuna 15, ‘yan sanda suka zo wurin da abin ya faru suka kubutar da ni aka kai ni wata cibiyar lafiya a wani kauye da ke kusa.

Sai dai Bakyasuwa ya bayyana cewa yana zargin wasu ‘yan siyasa ne ke daukar nauyin maharan, saboda a cewarsa a watannin baya wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan direbansa a Gusau kan hanyarsa daga Command Guest-Inn zuwa Anguwar Gwaza suna tafiya da motar ofishinsa.

Sai dai shugaban yana kira ga hukumomin tsaro da su kawo masa agaji, domin rayuwasa na cikin hadari Kuma ya bukacesu dasu gudanar da kwakkwaran bincike don kama wadanda suka kai masa harin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *