Kwamitin Tsaftace Ayyukan Yan Masana’antar Kannywood Sun Yi Nasarar Rufe Guraren Shirya Fina-finai Uku Da Kama Diraktoci Biyu, Da Wasu Jarumai Da Kuma Sauran Wadanda Suke Aikin Shirya Fina-finai Guda Talatin.
Shugaban Kwamitin tsaftace ayyukan yan Masana’antar kannywood wanda Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano ta kafa domin tabbatar da ana bin dokokinta sau da kafa karkashin Tijjani Asasi ya ce kwamitin ya sami nasarori a yayin gudanar da ayyukansa wanda suka hada da rufe guraren da ake shirya fina-finai ba bisa ka’ida ba har guda uku tare da kama Diraktoci biyu da sauran ma’aikata da jaruman masana’antar ta kannywood har talatin.
Alfijir labarai ta ruwaito Tijjani Asasi na bayyana hakan ne ga Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano, Abba El-mustapha yayin da Kwamitin yake bayyana wani bangare na rahoton wasu daga cikin nasarorin ayyukan da suka Sami tun bayan nada su a matsayin shuwagabanni.
Da yake nasa jawabin shugaban Abba El-mustapha ya jinjinawa Shugaban Kwamitin tare da ‘ya’yan kwamitin duba da yadda suka jajirce wajan sauke nauyin da Hukumar ta dora musu duba da cancantarsu tare da kishin da suke da shi na ganin Hukumar da Masana’antar ta kannywood sun sami cigaba mai dorewa.
El-mustapha ya jaddada cewa ba’a kafa kwamitin dan aciwa kowa mutunci face tsaftace fito da kima da daraja ta Masana’antar kannywood inda ya kara da cewa manufar kafa kwamitin ita’ce tabbatar da ana bin doka da ka’ida a Masana’antar kannywood sau da kafa.
Shugaban Hukumar ya mika sakon godiyarsa ga yan masana’antar kannywood da A’lummar Jahar Kano baki daya dangane da goyan baya da hadin kan da suke bawa Hukumar a koda yaushe.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj