
Alfijr ta rawaito Manchester United ta lashe kyautar bajinta uku a gasar Premier League a watan Fabrairu.
Erik ten Hag shine ya lashe kyautar mai horarwa da ba kamarsa a watan Fabrairu, wanda ya yi takara da Antonio Conte na Tottenham da Marco Silva na Fulham.

Kungiyar Old Trafford ta buga wasannin Premier League a cikin watan Fabrairu ba tare da an doke ta ba.
Kwazon da Ten Hag ya lashe kyautar a watan Satumba, wanda ya fara aiki a United tun kan fara kakar bana.
Shi kuwa Marcus Rashford shine ya karbi kyautar dan wasan da ba wanda ya kai shi taka rawar gani a watan na Fabrairu.

A cikin watan ne ya ci kwallo biyar daga wasa hudun da ya buga har da wadda ya zura a ragar Crystal Palace da Leicester City da kuma Leeds United.
Golan United, David de Gea shine aka bai wa wanda ya tare wata kwallo da ya kamata ta fada raga a wasan Premier League da Leicester City.
Kwallon kuwa ita ce wadda Kelechi Iheanacho ya buga masa a karawar da United ta ci 3-0 a Old Trafford..

Kyautar da aka bai wa De Gea sabuwa ce a kakar 2022/23, ya zama na farko da ya karba, wadda za ake karrama kwazon gololi a Premier League.
BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai