Labari Mai Daɗi: Gwamnatin Kano Za Ta Maida Gidan Yarin Kurmawa Cibiyar Tarihi Da Raya Al’adu

FB IMG 1754266749145

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana kudirinta na sauya fasalin gidan gyaran hali na Kurmawa da ke tsakiyar birnin Kano, inda za ta mayar da shi cibiyar adana tarihi da raya al’adun gargajiya na jihar.

Sanarwar hakan na kunshe ne a wani sako da Babban Mai Taimaka wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan kafafen sada zumunta, Salisu Yahaya Hotoro, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

A cewarsa, gwamnati za ta kwashe dukkanin fursunonin da ke Kurmawa zuwa sabon gidan yari na Janguza, tare da mayar da tsohon ginin Kurmawa cibiyar yawon buɗe ido da ke kunshe da kayan tarihi da fasahar gargajiya.

Ya kuke ganin wannan kudirin?

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *