Labari Mai Dadi! CBN Ya Sake Karya Farashin Dala A Najeriya

Screenshot 2024 02 27 13 29 28 70 b86672daa061159f52c1a3195c773d05 edit 485116325967

Babban Bankin Nigeria CBN ya sake sanar da matakin karya farashin dala daga N1,251 zuwa N1,101.

Alfijir  Labarai ta rawaito ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da darakta a sashen musayar kuɗi na bankin, Dakta Hassan Mahmud ya sanyawa hannu.

Sanarwar ta ce bankin ya tsara sayar da dala miliyan 15.88 ga ƴan canji 1,588 da suka cancanta.

A cewar sanarwar, su kuma ƴan canji ana sa ran su ci ribar da ba ta wuce kashi 1.5 ba cikin 100.

Hakan na nufin za su sayar da dala ɗaya ne a kan N1,117.

Sanarwar na cikin matakan da CBN ke ɗauka domin daidaita kasuwar musayar kuɗi a Najeriya da kuma tabbatar da gaskiya da bin doka a tsakanin masu canjin kuɗi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *