Idan da sauran ‘yan majalisa da jami’an gwamnati za su iya gudanar da tallafi makamancin hakan da an sami saukin rayuwa
Alfijir Labarai ta rawaito Dan Majalisar Wakilan Mazabar Jere ta jihar Barno, a majalisar Wakilai, Ahmed Satomi, ya ba da kwangilar gidajen mai guda 15 don sayar da mai ga masu sana ar haya da ababen hawa a kan Naira 430 kan kowace lita.
A halin yanzu ’yan kasuwa na sayar da man fetur tsakanin Naira 635 zuwa 655 kan kowace lita a Maiduguri babban birnin Jihar Borno.
“An ba da kwangilar ne a gidajen mai guda 15 domin su sayar da lita 37,500 na man fetur a kan Naira 430 kan kowace lita,” inji shi.
Satomi, wanda ya samu wakilcin shugaban kwamitin kula da harkokin man fetur, Nur Lawan, ya lura da cewa “Yanayin tattalin arziki ya tilastawa da yawa daga cikin masu baburan adaidaita da sauran su, barin kasuwanci, don haka ba za su iya ciyar da iyalansu ba,” in ji shi.
Ko’odinetan hukumar kula da harkokin man fetur ta Satomi Muhammed Alhaji Muhammad ya ce matakin da dan majalisar ya yi shi ne kashi na farko, “sauran matakan na nan tafe”.
Daya daga cikin ma’aikatan Keke Napep Abdullahi Mohammed, ya ce shiga tsakani ya nuna yadda masu rike da madafun iko ke son rage musu radadin da suke ciki.
“Idan da sauran ‘yan majalisa da jami’an gwamnati za su iya gudanar da tallafi makamancin hakan, da an sami saukin rayuwa, za mu ci gaba da zuba jarin mu, kuma mu gudanar da harkokin kasuwanci a kan farashi mai rahusa, suma fasinjojinmu za su sami saukin caji, ”in ji shi.
A makon da ya gabata, Daraktocin Hukumar Tsaro ta Jiha na Jihohi shida na Arewa maso Gabas sun gana tare da duba matsalolin tsaro a shiyyar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@musa_bestseller
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM