Labari Mai Dadi! Gwamnan Kano Ya Sanya Hannu A Dokar Gwajin Lafiya Kafin Aure A Kano

IMG 20240507 WA0098

Gwamnan Abba Kabir Yusuf, ya amince tare da sanya hannu ga dokar gwajin lafiyar ga wadanda suke shirin yin aure a jihar Kano a hukumance, wadda ta tanadi duba lafiyar duk masu son aure.

Alfijir Labarai ta rawaito sabuwar dokar tace ba za a yi aure a Kano ba tare da ba da takardar shaidar lafiyar jinsin halitta, hepatitis B da C, da HIV/AIDS, da sauran cututtuka masu alaka da su.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24, ya ce dokar tace ya zama dole a yi hakan domin rage haihuwar yara masu fama da matsalolin lafiya kamar su sikila HIV/AIDS, da ciwon hanta.

Wannan shiri dai ya yi daidai da kudurin gwamnan jihar Kano na inganta da samar da yanayi mai kyau ga fannin kiwon lafiya, da nufin ganin Kano ta kubuta daga matsalolin kiwon lafiya ko kuma rage radadin.

Dokar ta wajabta yin gwajin tilas na HIV/AIDS, Hepatitis, genotype, da sauran abubuwan da suka dace kafin aure.

A lokacin rattaba hannun kan dokar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa manufar aiwatar da dokar ita ce don rage yaduwar wasu cututtuka ga yaran da za’a haifa.

Dokar ta bayyana cewa duk wanda aka samu da laifin saba wa dokar, zai iya fuskantar tarar Naira dubu dari biyar, na tsawon shekaru biyar, ko kuma duka biyun.

IMG 20240507 WA0099
Kano State

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *