Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umaru Radda ya amince da bai wa ma’aikatar jihar goron sallah a naira 15,000.
Alfijir labarai ta rawaito cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa na X, ya ce sakamakon yanayin matsin rayuwa da ake ciki, ya amince da bayar da naira 45,000 ga ma’aikatan jihar da na ƙananan hukumomi.
”Sai dai naira 30,000 daga cikin kuɗin zai kasance bashi ne gwamnati ta ba su, wanda kuma za su biya cikin wata uku masu zuwa, inda za a riƙa cire naira 10,000 a cikin albashinsu a kowane wata daga Yuli zuwa Satumba”, in ji sanarwar.
Gwamna Dikko Radda ya ce ya yi hakan ne domin bai wa ma’aikatan jihar da ya kira ”haziƙan ma’aikata” su samu damar gudanar da shagulgulan bukukuwan babbar sallah cikin walwala, duba da halin matsin rayuwa da ake ciki.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj