Daga SADIQ I. MUHAMMAD LARA
An gudanar da taron tsoffin daliban a cikin Makarantar gidan makama dake kofar kudu Gidan Sarkin Kano tare da murnar cikar makarantar shekaru 90 da kafuwa.
Alfijir labarai ta rawaito taron wadanda ya sami halartas manyan Mutane kamar su….
~Mal. Ibrahim Shekarau
~General Magashi
~Hon Nura Hussain
~Hon. Umar haruna doguwa
~Baffa Babba Dan agundi
~Mai girma Walin Kazaure
Da sauran mutane daban-daban daga fadin Kano da Jigawa.
Yayin gabatar da taron Hon. Nura Hussain na daya daga cikin tsofaffin daliban wannan makarantar, kuma ya nuna farin cikinsa da wannan ranar sannan ya fanshi calender da aka gabatar akan kudi Naira miliyan biyu. ₦2,000,000
Hon bai tsaya a nan ba sai da ya bada kudi Naira miliyan daya ₦1,000,000 domin a rabawa malaman da suka koyar dasu a wancan lokacin.
Hakazalika Hon Nura Hussain yayin alkawarin za a karawa headmaster na makaranta girma saboda kokari da jajircewarsa wajen kawo cigaba a makarantar.



Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V
Allah ya bada abun akenema na Alkhairi