Labari Mai Dadi! Tinubu Yayi Umarnin Buɗe Iyakokin Najeriya Da Nijar

Screenshot 20240313 154139 com.android.chrome edit 4206205774356

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bayar da umarnin sake buɗe kan iyakokin ƙasar – ta sama da ta ƙasa – da jamhuriyar Nijar.

Alfijir labarai ta rawaito kakakin shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce shugaban ya buƙaci a buɗe iyakokin nan take ba tare da ɓata lokaci ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa shugaba Tinubu ya ɗauki matakin ne sakamakon taron ƙoli na kungiyar ECOWAS da aka gudanar a ranar 24 ga Fabrairu, 2024, a Abuja, inda shugabannin suka amince da ɗage takunkuman tattalin arziki da aka kakaba wa wasu ƙasashen ƙungiyar, ciki har da jamhuriyar Nijar.

Ana sa ran ɗage takunkumin zai rage zaman ɗar-dar da bunƙasa harkokin kasuwanci da tattalin arziki tsakanin Najeriya da ƙasashen da ke makwabtaka da ita.

Umurnin da shugaba Tinubu ya bayar ya kunshi matakai daban-daban da nufin maido da alakar da ke tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

Daga cikin takunkuman da aka ɗage sun hada da “Buɗe iyakokin ƙasa da na sama tsakanin ƙasashen biyu, da kuma na hana zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci da ke shiga da kuma fita daga Nijar.”

Haka kuma Najeriya ta sanar da ɗage takunkumin hana bai wa Jamhuriyar Nijar wutar lantarki da a baya ta yi.

“An kuma ɗage dokar hana hada-hadar kasuwanci da hada-hadar kuɗi tsakanin Najeriya da Nijar, tare da riƙe kadarorin ƙasar Nijar da ke babban bankin ECOWAS da kuma bankunan kasuwanci.” a cewar sanarwar.

Bugu da ƙari, umarnin na shugaba Tinubu ya ƙunshi ɗage dokar hana zirga-zirga da aka sanya wa jami’an gwamnati da ƴan’uwansu daga Nijar.

Wannan matakin na nuni da aniyar yin huldar diflomasiyya da inganta huldar lumana a yankin ECOWAS.

Haka kuma, matakin ɗage takunkumin kuɗi da tattalin arziki da aka ƙaƙaba wa Jamhuriyar Guinea ya nuna goyon bayan Najeriya ga ƙoƙarin daidaitawa da dawo da zaman lafiya a yankin.

Sanarwar ta jaddada muhimmancin waɗannan ayyuka wajen inganta haɗin kai da haɗin gwiwa a yankuna.

Ana sa ran dage takunkumin da aka ƙaƙaba wa ƙasashen Nijar da Guinea zai taimaka wajen dawo da harkokin tattalin arziki yadda ya kamata da kuma samar da zaman lafiya da ci gaban yankin ECOWAS baki daya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *