Labari Mai Dadi! Wasu Ƙwararrun Masu Haɗa Wa Boko Haram Bam Sun Miƙa Kansu Ga Jami’an  Tsaro

Screenshot 20240423 093021 Facebook

Wasu ƙwararrun masu haɗa bama-bamai, IED, na Boko Haram su biyu, Abubakar Mohammed da Bana Modu, sun mika wuya ga dakarun rundunar hadin gwiwa ta MNJTF a Borno.

Alfijir Labarai ta ruwaito Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi, babban jami’in yada labarai na soji –Ndjamena ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri a jiya Litinin.

Ya ce wadanda ake zargin ƴan kasa da shekaru 30 sun mika wuya ne a wani samame da sojojin suka yi a ranar Lahadi, 21 ga watan Afrilu.

Abdullahi ya ce an kwato bama-bamai guda biyu, wayoyin hannu biyu da kudi Naira dubu 53 daga hannunsu.

Ya ce da ake yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun ce kwamandojinsu na Boko Haram ne suka umurce su da su dasa bama-bamai a kan hanyoyin Doron Baga da kuma gonar kifi a Baga, dukkansu a karamar hukumar Kukawa ta jihar.

“A maimakon aiwatar da aikin nasu, sai suka yanke shawarar yin watsi da aikin nasu, su tsere da bama-baman da kuma mika wuya ga MNJTF.”

Ya kara da cewa miƙa wuyan na su na da nasaba da sabon salon yaki da ta’addanci da rundunar ta ɓullo da shi na gyaran tunanin ƴan ta’addan ba ta amfani da karfin bindiga ba mai taken ‘Operation NASHRUL SALAM’.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *