Wata baturiya, yar ƙasar Bulgaria, Liliana Mohammed ta yi saukar Alqur’ani mai girma a Jihar Kano.
Alfijir labarai ta rawaito cewa aure ne ya kawo Liliana, mai shekaru 62 zuwa garin Kano, yanzu tana da shekaru 30, bayan da ta auri wani da kasuwa dan jihar, Marigayi Alhaji Ibrahim Sambo.
Da ta ke zanta wa da manema labarai, Liliana ta ce ta musulunta ne shakaru goma da suka gabata, inda daga nan ta fara koyon karatun Alkur’ani.
A cewar ta, ta fara koya ne a gida, duba da shekarunta, a karkashin wata Malama mai suna Malama Hafsa.
Kamar wasa, a cewar ta, sai gashi ta yi bikin sauka a ranar Asabar a wata makaranta mai suna Mamba’irrahman Islamic School a cikin birnin Kanon Dabo.
“Na ji dadi da na karbi Addinin Musulunci. Ina samun farinciki da kwanciyar hankali. Sannan saukar Alqur’ani din nan ma ta bani farinciki.
“Alqur’ani littafi ne mai dadi kuma shine ya ke zame min jagora a rayuwa ta a halin yanzu. Zan ci gaba da kokarin yin hadda, duk da cewa dai na tsufa,” in ji Liliana, mai ƴaƴa biyu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp