Ma’aikatan Zaɓe Da Ƴan Jarida Sun Sha Da Ƙyar A Wata Mazaɓa A Kano

Alfijr ta rawaito Rahotanni daga Jihar Kano sun bayyana cewa an samu wata hatsaniya a mazaɓar Ja’oji har wasu ma’aikatan zaɓe da ƴan jarida suka sha da ƙyar.

Wakilin BBC wanda ya kasance cikin ƴan jaridar da suka ɓuya a wani aji tare da malaman zaɓe, ya bayyana cewa ɓatagarin sun kutsa cikin mazaɓar ne a dai-dai lokacin da jami’an INEC ke shirin fara ƙirgen ƙuri’u bayan da aka kammala zaɓe a mazaɓar.

Lamarin dai ya sa dole aka dakatar da aikin har zuwa lokacin da lamarin ya lafa.

Wakilin na BBC ya tabbatar da cewa mutanen da ke mazaɓar sun nemi mafaka a wata makaranta a lokacin da suka ga ɓatagarin.

Ya ce ya hango ƴan daban ɗauke da muggan makamai sun kai kawo a mazaɓar, inda ya ce sun tafi da na’urar VBAS guda ɗaya daga mazaɓar.

A cewarsa, jami’an tsaro ba su isa wajen ba a lokacin da ɓatagarin suka shiga mazaɓar.

Tuni dai aka samu lafawar al’amarin inda kuma aka soma ƙirgen ƙuri’un a wannan mazaɓa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *