Magu ya bankaɗo damfarar Dala biliyan 11 da aka nemi yi wa Najeriya a harkar P&ID

📸EFCC

A cikin kwangilar, an amince Najeriya za ta riƙa bayar da gas tsawon shekaru 20, shi kuma P&ID zai gina masana’antar.

Ranar Litinin Babbar Kotun Landan ta soke hukuncin da a farko wata kotu ta nemi Najeriya ta biya Dala biliyan 11 ga kamfanin P&ID, saboda karya yarjejeniyar kwangila.

Mai Shari’a ya gano cewa an bayar da kwangila ta hanyar zamba, ba bisa ƙa’ida ba.

Babban abin da ya kawo samun wannan nasara a Kotun Landan a ranar Litinin, shi ne wani binciken da EFCC a ƙarƙashin tsohon shugaban hukunar, Ibrahim Magu ta bankaɗo, inda aka gano cewa kwangilar ma ba bisa ƙa’ida aka bayar da ita ba. Don haka batun a biya diyya bai ma taso ba.

Farkon Harƙallar: Tun cikin 2010 ne kamfanin Precess & Industrial Development Ltd (P&ID), ya samu kwangila daga Ma’aikatar Harkokin Fetur, wadda zai gina babbar masana’antar gas, a Kalaba, babban birnin Jihar Kuros River.

A cikin kwangilar, an amince Najeriya za ta riƙa bayar da gas tsawon shekaru 20, shi kuma P&ID zai gina masana’antar.

Sai dai kuma Najeriya ba ta bayar da gas ɗin ba, kamar yadda ta yi alƙawari, shi kuma P&ID bai gina masana’antar ba.

Daga nan sai P&ID ya maka Gwamnatin Najeriya a kotu, kan laifin karya yarjejeniyar kwangila. Ya shigar da ƙarar a kotun sasanta ja-in-jar kwangiloli a Ingila.

Cikin 2017 sai kotun ta bai P&ID nasara, cewa a biya kamfanin diyyar Dala biliyan 6.6 tun a wancan lokacin, adadin da a yanzu ya kai Dala biliyan 11 kenan, saboda kuɗin ruwa da ya riƙa ƙaruwa.

Ƙoƙarin Magu A EFCC Ya Bankaɗo Harƙallar Kwangila:

Cikin 2016 tsohon Shugaban EFCC, Ibrahim Magu, ya nemi amincewar Shugaban Ƙasa na lokacin, Muhammadu Buhari da Mataimakin sa, Yemi Osinbajo, inda ya duƙufa binciken kwangilar, wadda ya gano cewa harƙalla ce kawai da badaƙala a tattare da kwangilar.

Abin takaici, daga baya an sauke Magu tare da tozarta shi, bayan ya bankaɗo wannan harƙalla. Kuma har yau an kasa bayyana takamaimen dalilin cire Magu daga EFCC.

Magu da EFCC sun gano yadda lauyan Ma’aikatar Fetur, Grace Taiga ta karɓi toshiyar baki daga P&ID.

Kuma EFCC ta zargi Taiga da aikata ba daidai ba, da kuma wani laifin ƙoƙarin haɗa baki a yi gagarimar harƙalla.

Haka nan EFCC a lokacin Magu ta gano tsohon Ministan Harkokin Fetur na lokacin, wanda yanzu ya rasu, ya sa wa kwangilar hannu ba tare da bin hanyoyi da matakan tantance kwangila ba.

Gwamnatin Najeriya da ta ga abin da EFCC ta bankaɗo, sai ta maka P&ID kotu a ranar 19 Ga Satumba, 2019, a Najeriya, bayan EFCC ta bankaɗo zamba da ƙoƙarin kauce wa biyan haraji da harƙalla a ɓangaren P&ID.

Haka kuma a Babbar Kotun Najeriya an kama P&ID har da laifin karkatar da kuɗi a asirce da kuma yin hada-hada ba tare da mallakar lasisin amincewa daga gwamnatin Najeriya ba.

Binciken da EFCC ta yi ne Najeriya ta tattara, ta garzaya Kotun Landan, wanda ya yi sanadiyyar a ranar Litinin kotun Landan ta ta yi watsi da buƙatar P&ID da ta nemi Najeriya ta biya ta diyyar dala biliyan 11, a wannan lokacin da ake fama da raɗaɗin tsadar rayuwa.

A ranar Litinin, Mai Shari’a Robin Knowles ya tabbatar cewa rahoton EFCC wanda ya bankaɗo yadda P&ID ya bai wa Taiga lauyar Ma’aikatar Harkokin Fetur ɗin Najeriya kyautar Dala 5,000 har sau biyu, gaskiya ne.

Knowles ya ce, An bai wa P&ID kwangilar ta hanyar harƙalla, kuma an saɓa wa dukkan ƙa’idojin da doka ta tanadar.”

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana wannan nasara da Najeriya ta samu a Kotun Landan cewa wata babbar guduma ce aka rafka kan bisa kan ‘yan harƙalla da masu maida Afrika saniyar-tatsar-dukiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KpTjEvHUjd3CVzIQp8CSkZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *