Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana ranar 25 ga watan Nuwamba ne a matsayin Ranar Yaki da Cin Zarafin Mata domin tunawa da sadaukarwar ‘yan uwansu mata Mirabal Sisters, waɗanda aka kashe a shekarar 1960, saboda gwagwarmayar su na kare hakkin mata a Dominican Republic.
Wannan rana na nufin jawo hankalin duniya kan illolin cin zarafi da kuma samar da mafita don kare mata daga wannan tsangwama.
Sai Kuma batun Hanyoyin Dakile Cin Zarafin Mata
A matsayinmu na masu kare hakkin bil’adama, muna ganin akwai matakai masu mahimmanci da za a bi don dakile cin zarafin mata:
1. Ilimantar da Al’umma: Ta hanyar wayar da kan jama’a game da hakkin mata kamar yadda Sashe na 1, 3 da 5 na Kundin Ƙasa da Ƙasa na Kare Hakkin Dan Adam (UDHR) ya tanada, wanda ya tabbatar da mutunci da ‘yancin kowanne dan Adam.
2. Kafa Dokoki da Hukunta Masu Laifi: Doka tana kare mata daga duk wani cin zarafi (Sashe na 7 da 8 na UDHR).
3. Tallafa wa Mata da Shirin Fadakarwa: Akwai bukatar kafa cibiyoyin tallafi don wayanda suka tsira daga cin zarafi su samu damar dawowa cikin al’umma lafiya.
4. Sanya Kungiyoyin Addini da Al’adu: Domin su taka rawa wajen gyara dabi’u na rashin mutunta mata.
Daga January zuwa yau 25 ga watan nuwanba mun samu Korafe-Korafe da yawa.
Bisa ga rahotannin ƙungiyar mu, daga watan Janairu zuwa yau (25 ga watan Nuwamba, 2024), an samu korafe-korafe guda 812 na cin zarafin mata a ƙasar nan.
Wadannan sun haɗa da batutuwa kamar fyade, barazanar aure, da wulakanci a wuraren aiki. Mafi yawan waɗannan laifuka sun faru ne a yankunan da matan ke da ƙarancin ilimi da kariya.
Muna son al’ummah tayi amfani da kuma lura da irinsu. Sashe na 3: Yana tabbatar da hakkin rayuwa da walwala.
Sashe na 5: Ya haramta azabtarwa ko wulakanci ga kowanne mutum.
Sashe na 16: Ya tabbatar da ‘yancin aure da samun kariya a cikin iyali.
Sashe na 19: Yana bai wa mata dama su bayyana ra’ayoyinsu ba tare da tsangwama ba.
Daga karshe. Muna sanar da al’ummah da duk masu fada aji cewa.Majalisar Dinkin Duniya ta ware wannan rana ce domin duniya ta fahimci muhimmancin kare mata daga cin zarafi da kyautata rayuwarsu.
Don haka, muna kira ga gwamnati, kungiyoyi, da al’umma baki daya su tabbatar da kare hakkin mata ta hanyar dabbaka dokoki da fadakarwa. Wannan zai taimaka wajen samun al’umma mai zaman lafiya da daidaito.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj