Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugaban karamar hukuma

Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugaban karamar hukumar Gwale Khalid Ishaq Diso na tsawon watanni uku.

Alfijir Labarai ta rawaito majalisar ta amince da rahoton kwamitinta kan harkokin kananan hukumomi da masarautu a zamanta na yau, Talata bayan zargin sayar da filayen gwamnati ba bisa ka’ida ba tare da daukar shawarwari ba tare da tuntuba ba.

Majalisar ta ce kansilolin 6 cikin 10 sun kai karar majalisar kan ayyukan shugaban da ba su ji dadin su ba.

Kakakin majalisar dokokin jihar, Jubril Ismail Falgore ya ce ana kuma zargin Diso da yanke shawara ta bai daya ba tare da daukar kansilolin ba.

Majalisar ta kafa wani kwamiti na wucin gadi da zai binciki zargin sannan ya bayar da rahoto nan da watanni biyu tare da umurci mataimakin shugaban majalisar da ya karbi ragamar mulki na tsawon watanni uku har sai an kammala bincike.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *