Majalisar Dokokin Kano Ta Tabbatar Da Tantance Sunayen Kwamishinoni 16

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban masu rinjaye na majalisar, Ismail Jibrin Falgore, a zaman majalisar a ranar Alhamis, ya ce an tabbatar da hakan ne kan kudirin da shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Husaini Dala ya gabatar wanda aka tattauna a gaban kwamitin baki daya bayan an tabbatar da su.

Wadanda aka tantance da majalisar ta tantance sun hada da:

Hon. Umar Haruna Doguwa,

Ali Haruna Makoda,

Dr. Abubakar Labaran Yusuf,

Danjuma Mahmud,

Musa sulaiman Shanono,

Abbas Sani Abbas,

Ladidi Garko,

Marwan Ahmad,

Muhd ​​Diggol.

Sauran sun hada da

Adamu Aliyu Kibiya,

Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata,

Safiyanu Hamza,

Tajuddeen Othman Ungogo,

Nasiru Sule Garo,

Barr. Haruna Isa Dederi

Baba Halilu Dantiye.

Solacebase ta tattaro cewa biyu daga cikin wadanda aka nada a matsayin kwamishinoni da har yanzu ba a tabbatar da su ba, sun tafi kasar Saudiyya suna gudanar da aikin Hajji, za a tantance su idan sun dawo kasar.

A halin yanzu dai majalisar ta kafa kwamitin tantancewa wanda zai dauki nauyin kafa kananan kwamitoci karkashin jagorancin shugaban majalisar, Ismail Jibrin Falgore.

kuma magatakardar majalisar Alhaji Ali Maje zai zama sakataren kwamitin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

One Reply to “Majalisar Dokokin Kano Ta Tabbatar Da Tantance Sunayen Kwamishinoni 16”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *