Majalisar Shari’ar Musulunci ta Najeriya (NSCJ) ta sanar da naɗin Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar a matsayin sabon shugaban majalisar, biyo bayan rasuwar tsohon shugaban majalisar, Sheikh AbdulRasheed Hadiyyatullah.
Sanarwar da sakataren majalisar, Malam Nafiu Baba Ahmed, ya fitar a yau Laraba, ta bayyana cewa Sheikh Bashir, wanda ke rike da mukamin mataimakin shugaba a baya, ya hau kujerar shugabanci kai tsaye bisa tsarin da ke akwai.
Sheikh AbdulRasheed Hadiyyatullah ya rasu ne a ranar Litinin da ta gabata yana da shekara 81 a jihar Osun, inda ya kwashe shekaru da dama yana jagorantar harkokin majalisar da kuma ba da gudummawa wajen ci gaban shari’ar Musulunci a Najeriya.
Majalisar ta kara da cewa za a sanar da sabon mataimakin shugaban majalisar a wani lokaci mai zuwa.
Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar, wanda aka nada shugaban majalisar, sanannen malami ne a fagen ilimin addini da kuma limamin masallacin Juma’a na Al-Furqan da ke jihar Kano. Ya shahara da ilimi mai zurfi da kuma kishin addinin Musulunci.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD