Alfijr
Alfijr ta rawaito Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) dake Kano a ranar Litinin, 25 ga watan Yuli, 2022 ta rantsar da sabbin dalibai sama da 500 da suka samu gurbin karatu na shekarar 2021/2022.
Kididdiga ta nuna cewa MAAUN Kano ita ce jami’a mai zaman kanta daya tilo daga cikin jami’o’i masu zaman kansu guda 111 da ake da su a Nijeriya da suka fara ayyukan karatu da dalibai kusan dubu daya a lokaci guda.
Alfijr
A jawabinsa, shugaban Jami’ar MAAUN Kano, Farfesa (Dr.) Mohammad Israr, ya ce taron na da matukar muhimmanci, domin bikin rantsarwar ya nuna cewa daliban da suka samu gurbin karatu a jami’ar a hukumance sun shiga shirin karatu bisa amincewar hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC)”.
“Cikin farin ciki nake yi wa daukacin dalibai barka da zuwa jami’ar, na yi imani cewa Allah zai yi amfani da wannan jami’a wajen bunkasar ku da ci gaban ku ta kowane fanni na rayuwa.
Alfijr
“Ina taya iyayenku murna kan babban rawar da suke takawa a rayuwar ku, ina addu’ar ka da wannan an kokarin na su ya tafi a banza,” in ji Shugaban MAAUN.
Shugaban ya ce Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya tana koyar kwasa-kwasai da ke da kimar kasuwanci ga dalibai yana mai jaddada cewa tsarin koyarwa a jami’ar ya shafi harkokin kasuwanci da kuma dogaro da kai.
“Saboda haka wadanda suka kammala karatu a wannan jami’a ba za su shiga jerin masu neman aikin yi ido rufe ba a kasar nan, za su kasance wadanda suka assasa da kuma shiga sahun gaba a harkokin kasuwanci nan da wasu shekaru masu zuwa,” in ji Farfesa Isar.
Alfijr
A cewarsa, MAAUN Kano jami’a ce da ta shafi dalibai domin wuri ne da zai iya gyara shugabannin da za su zo a gaba.
“Muna alfahari da horar da dalibai a ayyukan ilimi. Muna mai da hankali kan haɓaka halayen ɗalibanmu bisa tsammanin cewa idan sun kammala karatun, za su ba da gudummawa mai ma’ana ga bayanan ci gaba a duk faɗin duniya,” in ji shi.
Shugaban, wanda ya taya sabbin daliban murna da samun gurbin shiga bayan sun samu tantancewa da gwaje-gwajen jarrabawa, ya shawarce su da su yi koyi da malamansu ta hanyar nuna tarbiya da sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.
Alfijr
Ya kuma gargadi daliban da aka rantsar da su bi ka’idojin Jami’ar da kuma zama masu kyawawan halaye tare da sanya tufafi ta mutunci.
A nata jawabin, kwamishiniyar ilimi ta jihar Kano, Dakta Mariya Bunkure ta shawarci daliban da aka rantsar da su maida hankali wajen karatunsu, duba da irin makudan kudaden da iyayensu suka biya domin yin karatu a jami’ar.
Bunkure, wanda kuma memba ce a hukumar gudanarwar Jami’ar, ta gargadi daliban da su guji yin wani abu da zai iya bata sunan su da na jami’ar.
Alfijr
Ta yabawa wanda ya kafa jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa kafa jami’ar wadda ta kasance daya daga cikin mafi inganci a kasar nan.