
Alfijr ta rawaito Manchester United ta tabbatar da cewa ta soke yarjejeniyar ta da Cristiano Ronaldo.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da suka wallafa a shafukansu na sada zumunta.
“Cristiano Ronaldo zai bar Manchester United bisa yarjejeniya nan take.
Kungiyar ta gode masa saboda gagarumar gudunmawar da ya bayar a tsawon lokuta biyu a Old Trafford.
Wannan ya biyo bayan hirar da Ronaldo ya yi da Piers Morgan.
Kungiyar agaji ta jajayen aljannu ta wargaza kwantiragin dan wasan mai shekaru 37 watanni bakwai da komawarsa.
Haka kuma ba za su biya fam miliyan 16 da Ronaldo zai samu nan da watan Yuni 2023.
United ta yi amanna cewa Ronaldo ya keta sharuddan aiki tare da sukar masu kungiyar na Amurka, kocin Erik ten Hag, da kayayyakin kungiyar, abokan wasansa da kuma tsofaffin yan wasan kungiyar, ciki har da Wayne Rooney da Gary Neville.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ