Hukumar yaƙi da cinb hanci da rashawa ta Nigeria EFCC, ta musanta rahotanin da ke cewar ta wanke wasu mutane da ake zargin suna da hannu a almundahanar da ake zargin an tafka a ma’aikatar kula da jinƙan al’ummar ƙasar da ta yi sanadiyar dakatar da Betta Edu daga ministar ma’aikatar.
Alfijir labarai ta rawaito wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Dele Oyewale ya fitar a jiya Lahadi ta ce har yanzu hukumar tasu ta EFCC na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Sanarwar ta ce babu wani jam’i daga ma’aikatar kula da jinƙan Najeriya da aka gayyata don amsa bayanai a hukumar ko ita kan ta dakatacciyar ministan ma’aikatar Betta Edu,”Bamu wanke kowa daga almundahanar da ake zargin an tafka a ma’aikatar ba.
Kawo yanzu mun yi nasarar karɓo naira biliyan 32.7 da dala dubu ɗari 445 daga ma’aikatar. In ji sanarwar
Haka kuma ta ce kuɗaɗen da ta iya ƙarbowa na daga cikin kudaden da aka yi almundahanarsu daga cikin kudaden tallafin korona, da na bashin bankin duniya, da kudaɗen Abacha da aka karbo, dukkansu aka baiwa ma’aikatar kula da jinƙan al’ummar ƙasar.
Hukumar ta ce suna mayar da martani ne akan wasu bayanai da ake yaɗawa na cewar hukumar ta wanke wasu daga cikin wadanda suke bincika.
Wannan dai na zuwa ne bayan da hukumar ta EFCC a wata mujallar hukumar ta EFCC da mai magana da yawun hukumar Dele Oyewale ya aikewa da BBC a ƙarshen watan Maris ɗin nan, ta na mai ambato shugaban hukumar Ola Olukoyede, sun yi nasarar karɓo naira biliyan 30, sannan suna bin ciken wasu bankuna 50.