Masalaha: Tinubu ‘Ya umurci Ganduje, Da Duk ‘Yan APC na Kano Su Sasanta Da Kwankwaso.

FB IMG 1705911730775

Daga Aminu Bala Madobi

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje da duk ‘yan APC na Kano da su sasanta da Kwankwaso.

Alfijir labarai ta rawaito Tinubu ya yi wannan kiran ne a wata ganawa da ya yi da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na Kano kwanaki kadan bayan hukuncin kotun koli da ya tabbatar da zaben Abba Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano.

Shugaban ya yi kira ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar da su bi hanyar tattaunawa da daidaikun jama’a, kungiyoyi ko jam’iyyun siyasa domin janyo su cikin jam’iyyar domin bunkasa hadin kai, ci gaba da ci gaban jihar.

Umurnin da shugaban Tinubun ya bayar ya girgiza dukkan masu ruwa da tsaki a taron kuma da shugaban ya ce ko kuna da wani ra’ayi ne? Cikin gaggawa, duk suka amsa umarnin shugaban da amincewa.

Saidai Shugaban bai ji dadin daya daga cikin kiraye-kirayen da masu ruwa da tsaki suka yi na a nada dan takarar jam’iyyar gwamnan APC awani matsayin wanda hakan ya fusata fuskar shugaba Tinubu.

Wata majiya a wajen taron ta shaidawa POLITICS DIGEST cewa tuni aka mika wannan kiran ga manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar NNPP ciki har da gwamna kuma sun nuna sha’awarsu ta shiga jam’iyyar APC amma sun nemi a ba su karin lokaci domin tuntubar shugabansu na kasa Sen. Rabiu. Musa Kwankwaso.

Tayin da aka baiwa jam’iyyar NNPP kashi 50% na shugabancin jam’iyyar tun daga matakin akwati, mazabu, kananan hukumomi da jiha.

An kuma bukaci gwamnan idan ya tashi yin nade-nade ya daidaita domin zuba ‘yan jam’iyyar APC na asali.

Zuwa yanzu ba a tabbatar ko gwamnan da ubangidansa Sen. Kwankwaso za su amince da wannan tayin ba.

Wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibrin, dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a 2023 Nasiru Yusuf Gawuna, karamin ministan gidaje da raya birane Abdullahi Gwarzo, karamin ministan babban birnin tarayya Mariya Mahmoud Bunkure da tsohon shugaban majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa daga cikin wadanda suka halarci taron.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *