Minista Hannatu Musawa Ka Iya Rasa Mukaminta A Wata Sa’insa Da Hukumar NYSC

Hukumar ƴan yi wa ƙasa hidima (NYSC) ta tabbatar da cewa ministar fasaha, al’adu da tattalin arziƙin fikira, yanzu take yin bautar ƙasa.

Alfijir Labarai ta rawaito hukumar ta bayyana cewa Hannatu Musa Musawa ta saɓa dokarta na hana masu yin bautar ƙasa riƙe muƙamin gwamnati.

Darektan hulɗa da jama’a na hukumar ya tabbatar da cewa hukumar za ta ɗauki mataki a kan laifin da ministar ta yi.

Hakan na kunshe ne cikin wani zargin da ƙungiyar HURIWA ta yi na cewa ministar yanzu take yin bautar ƙasarta, yayin da take riƙe da muƙamin minista a gwamnatin Shugaba Tinubu.

Darektan hulɗa da jama’a na hukumar NYSC, Eddy Megwa, ya tabbatar da cewa ministar ƴar bautar ƙasa ce yanzu haka, cewar rahoton Daily Trust.

Darektan ya tabbatar da cewa ministar tana yin bautar ƙasarta ne a birnin tarayya Abuja, inda yanzu take cikin wata na takwas.

Hannatu Musawa ta saɓa doka, NYSC Megwa ya yi bayanin cewa riƙe muƙamin kujerar ministan da Hannatu Musawa take yi a yanzu haka ya saɓa doka.

Ya yi bayanin cewa saɓa dokar hukumar ne wani ko wata mai yin bautar ƙasa ya karɓi muƙami a gwamnati, har sai ya kammala shekara ɗaya na bautar ƙasa.

A cewar Megwa tun da farko an tura Hannatu jihar Ebonyi domin yin bautar ƙasa a shekarar 2001, amma daga baya ta dawo jihar Kaduna domin cigaba da yin bautar ƙasa.

Ya bayyana cewa lokacin da ta dawo jihar Kaduna ne ta tsere ba ta kammala bautar ƙasarta ba.

Megwa ya yi nuni da cewa hukumar za ta yi duba da idon basira kan lamarin domin ɗaukar matakin da ya dace.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *