kwamitin amintattu na MOPPAN Ya Sake kafa kwamitin riko na reshen jihar Kano.
Best Seller Channel ta rawaito cewar kwamatin amintattu na MOPPAN ta amince da nadin daya daga cikin mambobin kwamitin riko na jihar Kano, sanarwar da Sani Mu azu ya fitar a daren Juma a ya tabbatar da nadin Umar Gombe a matsayin sabon shugaban kwamitin riko na jihar Kano nan take domin dinke barakar da tsohon shugaban ya haifar.
Haka zalika kwamatin ya amince da nadin Haj. Asma’u Sani a matsayin karin mamba a kwamitin rikon kwarya da aka sake kafa domin baiwa kwamitin karin ma’auni na daidaiton jinsi a jihar kano.
Sauran membobin kwamitin riko sun hada da Yaseen Auwal, Saima Mohammad, kamal S. Alkali, Sulaiman Edita sun ci gaba da zama membobinsu.
Kwamatin amintattu ya ba da shawarar cewa idan wani daga cikinsu yana da sha’awar tsayawa takara a kowane matsayi na zaɓe, wannan memba ya kamata ya yi murabus da farko kafin ya bayyana aniyarsa.
A Cewar kwamatin ya dauki reshen jihar Kano a matsayin wani muhimmin babi kamar kowace jiha a karkashin MOPPAN da bai kamata a bar ta a baya ba domin abin da wani bangare ke yi, yana shafar wasu.
Kwamatin ya yarda cewa kwamitin riko na da ikon gudanar da zabe a jihar, saboda yana da cikakkiyar dama da kundin tsarin mulkin Kungiyar masu shirya wasan kwaikwayon ta samar.
Babban dalili da lokacin da aka baiwa kwamitin riko na Umar Gombe shi ne, shirya zaben jaha cikin kankanin lokaci cikin Aminchi.
Best Seller Channel
A karshe kwamatin amintattu na MOPPAN ta yi kira ga daukacin mambobin kungiyar da sauran masu ruwa da tsaki a jihar Kano da su bai wa sabon kwamitin da aka sake nada dukkan goyon baya da taimakon da ya dace domin samun nasarar gudanar da wannan gagarumin aiki da aka yi.
Taken da ita wannan kungiya kewa kanta a kullum shi ne:
Mu ‘yan kungiyar Motion Picture Practitioners’ Association of Nigeria, mun tabbatar da tsayuwar daka; MU HADU a karkashin inuwa guda domin amfanin babbar sana’ar mu; DA KUMA Samar da Kundin Tsarin Mulki don Inganta, haɓakawa da aiwatar da Hotunan masu motsi a Najeriya da kuma jin daɗin membobinmu.