Muhuyi Magaji Rimin Gado, shugaban hukumar korafe-korafen al’umma da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ya amince cewa an sayar da filin da aka sanya wa alamar rushewa.
Alfijir Labarai ta rawaito cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta sanyawa wasu kadarori alamar da za a rushe.
Daga cikinsu akwai filayen wasa da gidajen mai da ke kan titin BUK, da kuma kadarori da aka gina a kewayen tsohuwar birnin Kano (Badala).
Isma’ila Bello, daya daga cikin masu gine-ginen da ke titin BUK, ya bayyana cewa ya samu filin ne daga hannun shugaban hukumar yaki da cin hancu da rashawa ta jihar.
Dan kasuwar ya ci gaba da zargin gwamnatin da yin alamar rugujewar da ta yi a baya bayan nan, inda ya yi zargin cewa wasu kadarorin da aka yi wa rushewar an same su ne bisa ka’ida daga wasu mutane masu alaka da gwamnati mai ci.
A nasa bangaren Rimin Gado wanda shi ne wanda da ake zargi da sayar masa da filin, ya shaidawa Daily Trust cewa gwamnatin da ta gabata ce ta bashi filin, kuma ya samu ne saboda ya gamsu cewa ba haramun ba ne.


Ya ce filin bai kasance a cikin ko kusa da makaranta ko wurin ibada ba kuma bai shafi tsohuwar katangar ganuwar birnin Kano ba.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai kan batun kadarorin da gwamnati ta yi wa alamar rusawar a yammacin ranar Juma’a, dan kasuwar wanda shi ne Sakataren kungiyar BUK Haudi Properties, ya ce sun sayi filayen su ne inda suka gina shaguna daga hannun masu shugaban hukumar karbar Korafe-korafe Rimingado wanda a halin yanzu yake jagorantar aikin rusau din.
Isma’ila Bello, daya daga cikin masu gine-gine da ke kan titin BUK da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi wa alamar rushewa ginin kwanan baya, ya ce ya samu filin ne daga hannun shugaban hukumar karbar Korafe-korafe da yaki da rashawa na jihar, Muhuyi Magaji Rimingado.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇