Mun Shirya Tsaf Domin Nasarar Abba Gida-gida Ta Wucin Gadi Ce – Ganduje

Alfijr ta rawaito Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce zasu ƙalubalanci sakamakon zaben gwamnan Kano a kotun sauraren kararrakin zabe.

  Ya bayyana hakan ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai akan shawarwarin da zaɓaɓɓen gwamnan kano Abba Gida Gida ya baiwa masu gine-gine a filayen gwamnati da kuma bankuna da masu bada bashi.

Ganduje yace sun shirya tsaf don tafiya Kotu, don haka koda sabon zaɓaɓɓen gwamnan na kano ya fara tafiyar da gwamnati zata kasance ta wucin gadi ne, duba da kwarin gwiwar samun nasara a kotu.

Ya Kara da cewar yana maganganu kamar shi ne gwamnan kano yanzu! Ina so ya Sani cewa Shawarwarin da yake baiwa mutane basu da tushe ballantana makama.

Gwamnan mai barin gado yace zasu gudanar da taron majalisar zartarwa, daga nan ne zasu tattauna akan batun tare da fitar da sunayen wadanda zasu yi aikin don ganin an mika mulkin ba tare da wata matsala ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *