Mun Yi Nadamar Zaben Bola Tinubu — In Ji Dattawan Arewa 

FB IMG 1712825798625

Kungiyar Dattawan Arewa, NEF, ta bayyana nadamar ta ta goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a zaben 2023.

Alfijir labarai ta rawaito kakakin NEF, AbdulAziz Suleiman, Da yake magana yayin tattaunawa da jaridar Guardian, ya ce kuskuren zaben Tinubu ya koya wa yankin darasi mai ɗaci.

Sai dai ya ce a ci gaba, Arewa za ta ba da fifikon hadin kai da fahimtar juna wajen zaben shugaban ƙasa.

Suleiman ya ce: “Arewa ta yi kuskure wajen zaben Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa a 2023, kuma da wuya su sake maimaita kuskuren nan gaba.

“Sun koyi darasi daga kura-kuran da suka yi a baya kuma za su yi kokarin zabo dan takarar da zai iya hada kan kasar nan tare da gudanar da mulki domin amfanin ‘yan Najeriya baki daya.

“A nan gaba, Arewa za ta yi taka-tsan-tsan wajen zabar dan takarar shugaban kasa,” in ji shi

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

2 Replies to “Mun Yi Nadamar Zaben Bola Tinubu — In Ji Dattawan Arewa 

  1. Tun baaje ko inaba, Ai Son zuciyarku yajamaku. Yau kungane gaskiyar Hajiya Naja’atu kenan. Allah ya sakamana a kanku, Don kune kuka jawomana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *