Alfijr ta rawaito rundunar ƴan sanda a jihar Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutane 18 sakamakon hatsarin da wata babbar mota da ke jigilar fasinjoji da shanu suka yi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kebbi, Nafi’u Abubakar ne ya sanar da hakan a wata sanarwa a ranar Litinin, 16 ga watan Janairu, 2023.
Ya bayyana cewa hatsarin ya rutsa da wani direban babbar mota mai lamba No. SRP 442 XA, Jihar Neja, masu jigilar fasinjoji da shanu daga Unguwar Illela zuwa Legas.
Daga nan sai motar a mahadar Malisa ta fadi, lamarin da ya yi sanadin mutuwar shanu goma sha shida.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Da isa mahadar Malisa direban ya kasa sarrafa motar nan ta fadi.
Sakamakon haka, fasinjoji 42 sun samu raunuka daban-daban.
“Da samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ahmed Magaji-Kontagora, ya garzaya wurin da lamarin ya faru, inda aka kwashe wadanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Gwandu, domin yi musu magani.
“Wani likita a asibitin ya tabbatar da mutuwar mutane 18, yayin da sauran wadanda abin ya shafa ke karbar magani a halin yanzu.
“Hakazalika, shanu 16 suma sun mutu sakamakon hatsarin.”
Kwamishinan ‘yan sandan ya jajantawa iyalan mamacin tare da addu’ar samun sauki cikin gaggawa ga fasinjojin da suka jikkata.
“CP ya yi kira ga NURTW, NARTO da sauran masu amfani da hanyar da su tabbatar da cewa sun sanya isassun matakan tsaro a cikin motocinsu kuma su kasance da hankali yayin tuki, da nufin hana afkuwar lamarin nan gaba,” in ji shi.
“Ya kamata su kiyaye iyakar saurin gudu, su guje wa yin lodi fiye da kima, rashin kulawa, da kuma yin taka tsantsan yayin tuki.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
Allah ya jikansu ya sauran lafiya
Allah ya jikansu ya sauran lafiya