Mutane 9 Sun Mutu, 6 Sun Jikkata, Yayin Da Wata Mota Ta Faɗa Cikin Dam A Jihar Kano

Alfijr ta rawaito hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar fasinjoji 9 a lokacin da motar su ta shiga Ƙwace ta fada wani Dam din Fada, a karamar hukumar Gwarzo ta jihar.

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 6:45 na yamma.

Sanarwar ta ce hatsarin ya afku ne da wata mota kirar Golf mai dauke da fasinjoji 12 da suka taho daga Kano zuwa Katsina.

Hukumar kashe gobara ta isa wurin bayan awa daya da samun labarin afkuwar lamarin.

Kakakin ya bayyana hatsarin ya afku ne sakamakon wata matsala da wata mota ta tsaya a tsakiyar titin ba tare da saka wata alama da masu ababen hawa za su fahimci akwai wani abu ba.

Hatsarin ya faru ne lokacin da direban Golf din ya rasa yadda zai yi ya fada cikin dam din bayan ya bugi wani dutse da aka ajiye kusa da motar.

Shedun gani da ido sun ce motar da ya kamata ta dauki direba da fasinjoji hudu a hukumance, tana dauke da mutane goma sha biyar.

Sanarwar ta ce “A ranar Asabar 19 ga watan Nuwamba, 2022, hukumar kashe gobara ta jihar ta samu kiran gaggawa ta hannun Ali Mai Faci, da misalin karfe 18:45 na safe, kuma ya kai rahoton wani hadari da ya afku a hanyar na Fada dam Gwarzo LGA Dayi.

Hukumar ta isa unguwar da misalin karfe 19:10 na safe.

”Sun gano cewa, wata motar Golf da ba a san lambarta ba, wadda ta taso daga Kano ta nufi Katsina ta fada cikin dam Fada.”

”An kuma ceto mutane 12 daga jihar Katsina, wadanda ba a san sunayensu ba.”

Wadanda lamarin ya shafa ‘yan mata 2 ne ‘yan kimanin wata 6, mata 4 ‘yan kimanin shekaru 30, 28, 27 da 25, da kuma maza 6 ‘yan kimanin 48, 45, 42, 40, 35, da kuma mai shekaru 28 da haihuwa.’’

Sanarwar ta kara da cewa, bisa namijin kokarin da mutanenmu da masunta na yankin suka yi nasarar ceto mutane uku da ransu, yayin da mutane tara suka sume tare da kai dukkan wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa babban asibitin Gwarzo domin kula da lafiyarsu.

Likitoci sun tabbatar da rasuwar Mutane 9 ne daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su.”

Kamar yadda wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa, wani fasinja daya ya bata har yanzu, ana ci gaba da neman sa izuwa yanzu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *