
Alfijr ta rawaito Rundunar Yansandan jihar Katsina tayi nasarar cafke wata mata mai shekaru sha 18 da ake zargin ta da kashe dan kishiyarta ta hanyar jefata rijiya.
Matar mai suna Maryam Habibu dake zaune a kauyen Leko na karamar hukumar Danja ta jefa dan kishiyarta dan shekaru 4 rijiya biyo bayan sakinta da Baban yaron yayi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Gambo Isah, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a yayin wani hole, ya bayyana cewa an kama matashiyar uwar gidan ne a ranar 9 ga watan Nuwamba, 2022.
Ya kuma bayyana cewa ta fitar da yaron ne ta jefa shi cikin rijiya.
A cewar PPRO, Maryam da mahaifin wanda aka kashen sun kasance basa tare da juna.
Maryam wanda a zantawarta da manema labarai ta amince da aikata laifin, tana mai cewa kaddara ce kawai.
A cewarta, “Gaskiya ne na jefa yaron a cikin rijiyar da ya mutu amma an kaddara cewa zai mutu a ranar. Shi ya sa ya rasu.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ