Mutum 80 Sun Mutu A Turmutsutsun Rabon Kayan Sallah


Alfijr ta rawaito Mayakan ƙungiyar Houthi sun tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 80 a wani turmutsutsu da ya auku yayin rabon kayan ƙaramar sallah a Sanaa babban birnin Yemen.

Ɗaruruwan mutane ne ciki har da ƙananan yara suka taru a wata makaranta domin karɓar tallafin kayan sallah.

Jami’an kungiyar Houthi da ke da iko da birnin sun ce lamarin ya auku ne a yankin Bab-al-Yemen.

Jami’an lafiya na daga ƙungiyar Houthi da ke iko da babban birnin na Yemen sun ce an garzaya da waɗanda suka ji raunuka da kuma waɗanda suka mutu zuwa asibiti a Bab-al-Yemen ɗin da ke tsakiyar birnin.

Hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yanayi na ruɗani da kuma gawawwakin yara duk
kwakkwance.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *