Na baiwa Dauda Gwamnan Jahar Zamfara amanar Sama da Dala Biliyan 9 – In Ji Diezani

IMG 20231224 WA0004

Diezani ta roki Tinubu da ya ba ta damar komawa Najeriya domin ta bayyana rashin da’ar da ta yi a lokacin da take mulki.

Alfijir labarai ta rawaito Diezani Madueke, tsohuwar ministar man fetur a zamanin Goodluck Jonathan, wacce ta tsere zuwa kasar Burtaniya saboda fargabar hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, ta roki gwamnatin shugaba Bola Tinubu da ya yi wa gwamnatin Najeriya sassauci.

Rahotanni sunce Diezami tana mataki na biyu na kamuwa da cutar daji ta roki Tinubu da ya ba ta damar komawa Najeriya domin ta bayyana rashin da’ar da ta yi a lokacin da take mulki.

“An zarge ni da laifin rashin da’a a lokacin da nake ministar man fetur, kuma gaskiya ne. Duk da haka, zan so Shugaba Bola Tinubu da ’yan Najeriya su gafarta mini, su bar ni na dawo gida, su ba da gudummawarsu, domin rayuwa na dawwama.”

Ta ci gaba da bayyana dangantakarta da Dauda Lawal Dare, gwamnan jihar Zamfara a halin yanzu, wanda ta ba wa sama da dala biliyan 9 don adanawa a lokacin da ya rike mukamin Babban Darakta na First Bank Nigeria PLC.

Ta ce, “Mijina da dukkan ’yan uwana da suka hada da lauyana dan Najeriya da ke da zama a Burtaniya sun san dangantakata da Dauda Lawal Dare, Gwamnan Jihar Zamfara a halin yanzu wanda na ba wa sama da dala biliyan 9 amanar tsaro a lokacin yana Babban Darakta. First Bank Nigeria PLC.

“Abin takaici, yanzu ya kai ga cewa Mista Dauda Lawal ba ya karbar kiran wayata, har ma ya yi aiki tare da hadin gwiwar ‘yan sandan Burtaniya don sanya min ido.

NEWS NG

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *