NDLEA Ta Kama Wata Mata Da Ɓoye Kilo 10.70 Na Tabar Wiwi Da Ake Shirin Kaiwa Ƙasar Qatar

FB IMG 1711907279967

An Damke matar ne da kilo goma na wiwi a filin jirgin Murtala Muhammed da ke Legas.

Alfijir labarai ta rawaito Jami’an Hukumar da ke Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi a Nijeriya NDLEA sun kama wata mata kan zarginta da yunƙurin fitar da ɗauri 20 na tabar wiwi.

A sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta ce matar mai suna Chidinma Chinenye Agbazue mai shekara 35 ta ɓoye kilo 10,70 na tabar wiwin a cikin salak da busassun ganyayyaki.

Matar wadda aka kama a filin jirgin Murtala Muhammmed da ke Legas, ta yi niyyar kai tabar wiwin birnin Doha na Qatar, in ji sanarwar.

NDLEA ɗin ta ce binciken farko ya nuna cewa Chidinma na zaune ne a Qatar amma ta koma Nijeriya Disamabar bara domin bikin Kirisimeti.

Hukumar wadda ta ce ta kama matar tare da haɗin gwiwar jami’an hukumar DSS, ta tabbatar da cewa Chidinma ta yada zango a otel ɗin Club Dice da ke Legas inda a nan aka miƙa mata wiwin.

Baya ga Chidinma, NDLEA ɗin ta ce ta kama Nwachukwu Chinedu mai shekara 28 a Jihar Abia kan zarginsa da safarar wiwi da tramadol.

“A Abia, an kama Nwachukwu Chinedu mai shekara 28 a ranar Juma’a 29 ga watan Maris a Akara Ahuba, Ƙaramar Hukumar Isikwuato. Abubuwan da aka gano daga hannunsa sun haɗa da kilo 46.65 na wiwi da adadi daban-daban na tramadol da methamphetamine da rohypnol da tsabar kuɗi N71,500,” in ji sanarwar.

Haka kuma NDLEA ɗin ta ce ta kama wata mota ƙirar Volkswagen kan hanyar Ondo ɗauke da kilo 127.5 na wiwi.

Hukumar ta ce akwai wata mai shekara 30 mai suna Chinasa Christopher wadda aka kama da kwalabe 400 na maganin tari mai ɗauke da kodin a Sabon Garin Kano.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *