Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), reshen Kano, ta bayyana cewar ta kama mutane 19 a wani gagarumin samame da ta gudanar a yankin Gezawa.
ASN Sadiq Muhammad Maigatari Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar NDLEA a Jihar Kano ne ya sanar da haka a wani jawabi da ya fitar yau Alhamis
Hukumar ta bayyana cewar ta rushe wuraren safarar miyagun kwayoyi ta kuma kwace tarin kwayoyi masu hadari a yayin samamen.
Maigatari ya kara da cewar, “Wannan aikin ya gudana karkashin jagorancin CN DY Lawal a matsayin wani bangare na shirin hukumar mai taken Operations Ramadan Mubarak”
Ya kuma ce samamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da ta samu daga wasu ‘yan kasa nagari, wanda ya taimaka wajen gano wuraren da ake gudanar da haramtattun ayyuka. Abubuwan da aka kwace sun hada da: Tabar-wiwi, dazapam Ezol-5, kwayar da ake kira sukudaye, sinadarin sholisho, pregabalin tablets da sauran kwayoyi masu hadari.
Ya tabbatar da cewar dukkan kayan da aka kwace yanzu suna hannun hukumar NDLEA yayin da bincike ke ci gaba.
CN DY Lawal ya bayyana cewa: “Manufarmu ita ce tabbatar da tsaron al’umma da kuma ba wa jama’a damar gudanar da azumin Ramadan cikin kwanciyar hankali. Idan wasu ba su damu da lafiyarsu da tsaron makwabtansu ba, to mu za mu dauki mataki don kare al’umma gaba daya. Muna maraba da hadin kan jama’a wajen bayar da sahihin bayanai domin kawar da wannan annoba.”
Jami’in Hulda da Jama’a ya kuma ce wannan aikin ya yi daidai da umarnin shugaban hukumar NDLEA na kasa, Brigediya Janar Mohamed Buba Marwa wanda ya umarci a ci gaba da gudanar da ayyuka ba tare da tsayawa ba domin dakile safarar da amfani da miyagun kwayoyi a fadin Najeriya.
NDLEA Kano ta jaddada cewa za ta ci gaba da yin aiki tare da al’umma wajen rushe hanyoyin safarar miyagun kwayoyi da kuma tabbatar da cewa masu aikata laifukan sun fuskanci hukunci.
Hukumar ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da rahoton duk wani abin da ake zargin ya shafi safarar miyagun kwayoyi. Bayanan sirri daga al’umma suna da matukar muhimmanci wajen kare lafiyar jama’a, tsaron iyalai da kuma tabbatar da zaman lafiya a unguwanni.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t