Shugaban hukumar, Farfesa Ibrahim Wushishi, ya bayyana haka a taron manema labarai a Minna, inda ya ce daga cikin ɗalibai 1,358,339 da suka zauna jarabawar, ɗalibai 818,492 ne, wato kaso 60.26 cikin ɗari, suka samu darussa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi.
Wushishi ya ƙara da cewa adadin ɗaliban da suka samu darussa biyar da sama ba tare da la’akari da Turanci da Lissafi ba ya kai 1,144,496, wanda ya yi daidai da kaso 84.26 cikin ɗari. Ya ce adadin masu laifi a jarabawar ya ragu zuwa 3,878 a bana, idan aka kwatanta da sama da 10,094 na shekarar da ta gabata raguwar kaso 61.58 cikin ɗari.
Haka zalika, makarantun da aka kama da laifi su 38 ne daga jihohi 13, yayin da malamai tara aka ba da shawarar a yi musu takunkumi.
A cikin jihohi kuwa, Kano ce ta zo ta farko da ɗalibai 68,159 da suka samu sakamako mai kyau, wanda ya kai kaso 5.020 cikin ɗari. Sai Lagos a matsayi na biyu da ɗalibai 67,007 (kaso 4.930 cikin ɗari) sannan Oyo ta biyo baya da ɗalibai 48,742.
Hukumar NECO ta kuma tabbatar da fara amfani da tsarin Computer Based Test domin rage jinkirin fitar da sakamako, tare da takaita darussa zuwa 38 kacal bisa sabon kundin karatu.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t