Nijar Za Ta Koma Amfani Da Tashoshin Jiragen Ruwan Kasashen Libiya Da Aljeriya

Nijar ta bayyana aniyarta na karfafa cinikayya da kasashe makwabtanta irin su Aljeriya da Libiya, ta yadda za ta yi amfani da tashoshin jiragen ruwan kasashen domin shigo da kayayyaki daga ketare ko kuma fitar da kayan kasar.

Alfijir labarai ta rawaito aniyar da gwamnatin ta Nijar ta kudiri yi na zuwa ne kwanaki bayan da kasar taki amincewa tare da kaurace wa shigo da kaya ta tashar jiragen ruwan Kwatonou da ke zama mafi kusa ga kasar.

Sai dai kungiyoyin ‘yan kasuwa sun yi lale marhabin da shirin, yayin da masana tattalin arziki ke ganin akwai bukatar yin taka tsan-tsan a cikin lamarin.

Kungiyar Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta sanya wa Nijar takunkumin karya tattalin arziki, sakamakon juyin mulki a ranar 26 ga watan Yulin shekarar da ta gabata da sojoji suka yi, wanda ya yi sanadiyyar rashin shigo da kayayyaki wajen amfani da tashar jiragen ruwan Kwatonou ta jamhuriyar Benin.

Saboda haka gwamnatin Nijar ta dukufa wajen samo sabbin hanyoyin da zasu saukaka shigo da kaya a cikin kasar ko fita da su zuwa kasashen waje.

Gwamnatin mulkin sojoji a Nijar ta sanar da shirin soma amfani da tashoshin ruwan kasashen Aljeriya da Libiya, domin shigo da kayayyaki cikin kasar.

Alhaji Habou Ali shine shugaban ‘yan kasuwa na kasar ta Nijar, ya bayyana jin dadinsu tare da yin lale marhabin akan wannan sabon shirin da gwamnatin ta bullo da shi.

Sai dai yayin da kungiyoyin ‘yan kasuwa ke murnar wannan shirin, masanin tattalin arziki, Aminu Ibrahim, na ganin akwai bukatar gwamnatin Nijar tayi taka tsan-tsan akan wannan lamarin, saboda akwai matsalar ‘yan ta’adda da ake fama da su.

Ibrahim ya ce dole ne sai an dauki mataki kwakkwara wanda zai tabbatar da daurewar alakar.

Gwamnatin kasar Nijar ta tura wata tawaga karkashin jagorancin Ministan Harakokin Wajen kasar Nijar zuwa kasar Libiya, inda suka tattauna da takwaran aikinsa a kasar da nufin inganta alakar da ke tsakanin kasashen biyu da ke makwabtaka da juna.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *