Nijeriya Ta Yi Gargadi Kan Yawan Samun Ruwa A Tankunan Mai Na Jiragen Sama

Daga Abdu Ado K/Naisa

Hukumar da ke sa ido kan sufurin jiragen sama ta Nijeriya NCAA ta koka kan yadda ake yawan samun ruwa a cikin tankunan jiragen sama, inda ta ce wannan babbar matsala ce.

Alfijir Labarai ta rawaito a ‘yan kwanakin nan, NCAA ta yi ta samun rahotanni daga kamfanonin jiragen sama da sauran masu aiki da jiragen kan matsaloli da ke da alaka da samun ruwa a cikin tankunan jiragen sama.

“Na baya-bayan nan shi ne rahoton ruwa mai yawa da aka zubar daga tankin wani jirgin sama kirar Boeing 737 wanda malejinsa ya burge yana tsaka da tafiya,” in ji sanarwar.

“Hukumar ta NCAA tana ganin ya zama dole sanin illoli da hadurran da ke tattare da zuba man jirgin sama da yadda za a shawo kansu kuma hakan yana da muhimmanci ga duk mutumin da ke sarrafa jirgin sama,” kamar yadda sanarwar ta kara da cewa.

Hukumar ta bayyana cewa sakamakon rashin bin ka’idoji yadda ya kamata, tana bukata cikin gaggawa kamfanonin jiragen sama da ma’aikatansu da dillalan man jiragen su kara inganta yadda suke zuba man jirgin kamar yadda aka tanada a daftarin tsarin zubawa da kula da man jirigin sama.

Hukumar ta ce hanyoyin da kamfanonin jiragen za su bi sun hada da ma’aikacin kamfanin jirgin sama da ke a kasa ya sa ido da kuma kula a lokacin da ake zuba man jirgin sama.

NCAA ta ce ya kamata ma’aikacin ya kula da tiyo da bututun zuba man har da taya da kuma gangar jikin motar da ta yi dakon man.

Haka kuma akwai bukatar a yi gwajin man domin tabbatar da cewa ko akwai ruwa a ciki ta hanyar daukar samfarin man kafin saka shi a jirgin saman da kuma bayan saka shi a jirgin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *