NNPCL ta durkusar da masana’antun man fetur da ci gaba da kashe kudin a banza da sunan gyara da kuma siyan kayayyaki a Najeriya
Alfijir labarai ta ruwaito tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana dalilin da yasa masana’antar man fetur na kasa ba ta aiki.
A cikin wata tattaunawa ta musamman da symfoninews a Abuja, tsohon shugaban ya ce alƙawarin gyara masana’antun man fetur na daurewa ne idan NNPC Limited na wasa da cigaba da cin hanci da rashawa.
A cewarsa, ƙoƙarin da gwamnatin sa ta yi na gyara masana’antar man fetur ya kasa cimma nasara saboda cin hanci da rashawa a cikin Kamfanin man fetur da suke yi a a lokacin mulkin sa.
Ya bayyana cewa NNPC na yaudar ‘yan Najeriya da ikirarin cewa za ta iya gyara masana’antar man fetur a zahiri ba haka bane.
Yace: “Lokacin da nake Shugaban Kasa, na kira manajan Shell su zo su taimaka mana wajen gudanar da masana’antar man fetur. Na gaya musu su dauki wani kaso a matsayin jari, amma sun ki yarda.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj