Fitaccen dan jarida kuma mai fashin baki kan al’amuran yau da kullum, Bash M Bash, ya bayyana cewa durkushewar harkokin masana’antu a Kano, shi ne ke haddasa koma baya a fannin kasuwanci da tattalin arzikin jihar.
Ya bayyana hakan ne yayin gudanar da Taron da kungiyar One Kano Agenda ta gabatar na karawa juna sani na kwana 2, aJami’ar Khalifa Isyaka Rabiu (KHAIRUN), da ke Kofar Gadon Kaya a cikin birnin Kano, ya kara da cewar rashin ayyukan masana’antu ya janyo koma baya ga harkokin sana’o’i da kasuwanci, tare da rage guraben ayyukan yi da kuma shigar kudaden shiga a jihar.
A cewarsa, idan har ana son Kano ta dawo matsayinta na cibiyar kasuwanci a Arewa da ma Najeriya baki daya, wajibi ne a farfado da masana’antu.
Ya yi kira ga manyan attajiran Kano, musamman Alhaji Aliko Dangote da Abdulsamad Rabiu (BUA), da su tashi tsaye wajen farfado da tsofaffin masana’antu da ke yankunan Sharada, Challawa da Dakata, domin su taka rawar gani wajen bunkasa tattalin arzikin jihar.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t