Rade-Radin Ficewa Daga PDP: Wike ya ziyarci shugaban APC Na Kasa

Daga Aminu Bala Madobi

Wannan dai na zuwa ne a lokacin da ake ta rade-radin cewa Wike, dan jam’iyyar PDP na shirin komawa jam’iyyar APC mai mulki.

Alfijir Labarai ta rawaito tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ziyarci sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Gnaduje, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

APC ta bayyana ziyarar ta Wike zuwa Ganduje ta shafinta na Twitter a ranar Talata, 15 ga Agusta, 2023.

Tsohon gwamnan na Rivers ya ziyarci Ganduje ne domin taya shi murnar zaben da aka yi masa a matsayin shugaban jam’iyya mai mulki ta kasa.

Wannan dai na zuwa ne a lokacin da ake ta rade-radin cewa Wike, dan jam’iyyar PDP na shirin komawa jam’iyyar APC mai mulki.

Wannan jita-jita na sauya sheka na kara ruruwa ne sakamakon kalaman magajin Wike, Gwamna Simi Fubara na jihar Ribas, jim kadan bayan hawansa mulki a ranar 29 ga watan Mayu, inda ya umarci Wike da kada ya watsar da shi.

Fitowar Wike a matsayin wanda aka nada a matsayin minista bai zo da mamaki ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *