Rashin adalci a shari’ar zaɓen Kano na iya haddasa tashin hankali – NNPP

FB IMG 1697408742655

Jam’iyyar adawa ta NNPP a Najeriya ta ce hana ta kwace mata zaben da ta ci a jihar Kano, zai iya janyo tashin hankalin da zai yaɗu zuwa sauran ƙasahen Afirka.

Alfijir labarai ta rawaito wata sanarwa da mukaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abba Kawu Ali, ya fitar, kuma babban jami’i mai binciken kuɗi na jam’iyyar, Ladipo Johnson ya karanta a gaban ofisoshin jakadancin Kasashen Yamma ranar Laraba, NNPP ta yi ikirarin cewa akwai alamun da ke nuna cewa ana yunkurin yi wa zaben mafi rinjayen al’ummar Kano zagon kasa.

‘Ya’yan jam’iyyar suna ci gaba da zanga-zanga a Kano tun bayan hukuncin kotun daukaka kara da ya sake tabbatar da soke nasarar gwamnan NNPP, Abba Kabir Yusuf.

A ranar Laraba kuma, magoya bayan jam’iyyar sun yi zanga-zanga zuwa ofisoshin Tarayyar Turai da ofishin jakadancin Amurka da na Birtaniya da kuma Hukumar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma (Ecowas).

Suna dai nuna ɓacin-rai ne kan hukuncin zaɓen gwamnan Kano da kotun korafin zaɓe da kuma ta ɗaukaka ƙara suka yanke a kan zaben gwamnan jihar Kano, da ya bai wa Nasir Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, gaskiya.

Ladipo Johnson ya ce tuni hankula suka tashi a Kano yayin da mutane ke ganin cewa an yi musu maguɗi a zaɓen 2019.

Ya ce jam’iyyar ba za ta yi wasa da ainihin takardar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara ba “kuma za mu yi duk abin da ya kamata bisa tsarin doka domin ƙwato abin da duniya ta sani cewa na mu ne.

“Yayin da NNPP ta garzaya zuwa Kotun Koli don bin kadinsu, mun damu da batun zama lafiya, musamman na jihar Kano da kuma arewacin Najeriya baki-ɗaya. Don haka, muna son Kotun Koli da ta yi adalci wajen dawowa da al’ummar jihar Kano da gwamna Abba Kabir Yusuf nasara.

“Yayin da muka tinkari kotun karshe, hankula sun tashi a Kano. Kowane lungu-lungu da sako na jihar na cike da ɓacin-rai, inda batun hukuncin kotun ya zama batun da ake tattaunawa a ko’ina, musamman kan tituna, ofisohi, da gidaje,” in ji NNPP.

NNPP ta ce tana son faɗa wa shugabannin duniya cewa abin da ake shirin yi ba abu ne mai kyau ga Najeriya kaɗai ba, har ma da Afirka da kuma duniya baki-ɗaya.

“Yunkurin kwace wa al’umma nasara a Kano zai haifar da sakamako kan al’amuran siyasa, tattalin arziki, da kuma rayuwar mutanen jihar,” in ji jam’iyyar.

Jam’iyyar ta kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki ciki har da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ƙungiyar gwamnonin Arewa, ƙungiyar sanatocin Arewa, ƙungiyar ƴan majalisar wakilai na Arewa, ƙungiyar shugabannin majalisun dokokin jihohi na Arewa, ƙungiyar kiristoci na Arewa, da kuma Malamai daga jihohi 19 na Arewa, da su janyo hankalin shugaban ƙasa da Kotun Koli wajen tabbatar da cewa an yi wa jam’iyyar da kuma al’ummar Kano adalci.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *