Rashin tsaro: IGP Ya Bada Umarnin Ba Sani Ba Sabo A Hanyar Abuja Kaduna

IMG 20240111 112437

Sufeto-Janar na ‘yan sanda (I-G), Mista Kayode Egbetokun ya bayar da umarnin a kara tura jami’ai a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna sakamakon karuwar fargaba a kan tsaro a hanyar.

Alfijir labarai ta rawaito wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a ranar Alhamis a Abuja, ya ce an tura dakarun ne domin inganta tsaro a yankin.

“Wannan na nufin yin amfani da fasahar ci-gaba da dabarun inganta hanyoyin samar da tsaro gaba daya,” in ji shi.

Egbetokun ya umurci mataimakin sufeto-Janar na ‘yan sanda (DIG) mai kula da ayyuka Mista Ede Ekpeji da ya kula da ma’aikatan da suka yi aiki a kan hanyar.

Shugaban ya ce an dauki matakin ne domin tabbatar wa ‘yan kasa da matafiya tsaron lafiyarsu, domin kara yawan jami’an tsaro a kan hanyar zai zama dakile masu aikata laifuka.

Ya bayyana bukatar hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da al’ummomin yankin da abin ya shafa, ya kuma bukaci jama’a da su kasance cikin taka-tsan-tsan, da bayar da rahoton abubuwan da ake zarginsu da kuma bayar da hadin kai ga jami’an tsaro.

IG ya ce kokarin hadin gwiwa yana da matukar muhimmanci wajen kiyaye tsaro da jin dadin mazauna da matafiya a kan hanyar.

Ya kuma jaddada cewa matakan wani bangare ne na kokarin ‘yan sanda na tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

(NAN)

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *