Rayuwata Na Fuskantar Barazana Da Tsoron Mai Zai Faru Gareni. Inji Jaruma Hadiza Gabon

Alfijr ta rawaito jaruma Hadiza Aliyu Gabon, ta yi ikirarin cewa rayuwarta na cikin haɗari saboda yadda ake fita da ita daga kotu a asirce a duk lokacin da aka zauna sauraron shari’arta.

Barista Mubarak Sani Jibril, shine lauyan jarumar ya bayyana hakan a gaban wata kotun shari’ar Musulunci a Kaduna a madadin jarumar.

Lauyan ya Kara da rokon kotun ta yafe wa jarumar halartar zaman sauraron ƙarar da aka kai ta, tun da tana da wakilci.

Alfijr

Ya kara da cewa taɓarɓarewar tsaro ya sa Hadiza Gabon cikin rashin kwaciyar hankali da fargabar abin da ka iya faruwa da rayuwarta idan ta ci gaba da halartar zaman kotun a kowane lokaci.

Lauya yaci gaba da cewar duk lokacin da Gabon ta halarci zaman kotun, sai dai a yi satar fita da ita.

“Rayuwata na cikin hadari, rayuwar mai karar ma na cikin hadari. Ba mu san wa ke bibiyar wannan sharia’ar ba a kafofin sada zamunta ba.

“Idan ba a yi hankali ba za mu iya ganin mutane dauke da bindigogi domin su sace mu.

“Wannan ita ce damuwarmu ba wannan shari’ar ba,” in ji Barista Mubarak Sani Jibril

Alfijr

Lauyan mai kara, Barista Naira Murtala, ya ki yarda da rokon lauyan jarumar, yana mai ikirarin cewa dole ne ta ci gaba da halartar zaman kotu.

Alkali Rilwanu Kyaudai, ya tabbatar musu da cewa kotun za ta yi la’akari da lafiyar mai kara da wacce a ke kara a zamanta na gaba.

Hadiza Gabon ta halarci zaman kotun ne a karar da wani ma’aikacin gwamnati mai suna Bala Musa ya kai karar ta a bisa zargin ta ki ta aure shi bayan ya kashe mata kudi Naira 396,000.

Alfijr

Sai dai kuma Gabon ta shaida wa kotu cewa ba ta ma san mutumin da ke wannan iƙirari ba.

Kamar yadda Radio Nigeria Kaduna ta wallafa