Rijiya Ta Bada Ruwa! Makomar Yan Kannywood A Gwamnatin Kano (KWANKWASIYYA)

FB IMG 1715723360859

Tun bayan samun nasarar Abba kabir yusif a matsayin gwamnan kano ake ta zuba idon aga shin wacce irin sakayya za’a yiwa yan masana’antar kannywood a gwamnatin kano, ganin yadda wasu masu akidar kwankwasiyya a cikin su suka bijirewa gwamnatin Ganduje mai ci tun daga matakin kasa har zuwa jiha.

Bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya sha rantsuwar kama aiki ne, sai yan film suka fara samun tagomashin mukami na shugabancin hukumar tace fina-finai wanda Abba El Mustapha ya samu,, daga nan kuma sai aka nada S A kannywood, Wanda aka baiwa Sanusi Oscar 442.

Daga nan sai aka sake bada kujerar MD Na gidan talibijin na ARTV wadda aka baiwa Hon Mustapha Adamu Indabawa. Sai kuma Fauzziya D Suleman da Maryam Jan Kunne da Aina’u Ade da suka sami tagomashin mukama. SA,

Wannan shine gatan dan Excellency Abba Kabir ya fara yiwa masana’antar Kannywood.

Ana tsaka da fara tafiya sai maganar Kotu ta kunno kai inda ta tsayar da komai a jihar. Bayan samun nasarar kotu ne hankula ya koma kan ganin shin wacce irin sakayya za a yiwa irin su Sani Danja, Yakubu Muhammad, Ty Sha’aban, Umar Uk, Salisu Officer da sauran wadanda aka san sun wahaltawa jamiyya sama da wanda ke rike da madafan iko.

FB IMG 1715723243902 1
Abba kabir yusif Da Sani Danja

Kwatsam sai kallo ya koma sama In da wani abun mamaki ya bullo na Fara ragewa yan kannywood karfi a cikin gwamnati.

A wani bincike da muka gudanar mun samu labarin fara shirin tsige shugaban talabijin din ARTV, sai kuma muka sake karo da korar producer Abdul aziz Dan small daga aikin da yake a ARTV, wanda gwamnatin Ganduje ce ta nadashi, amma duk akidar kwankwasiyyarsa a haka yake aikinsa, ita kuma gwamnatin ta hakura ta barshi.

IMG 20240514 WA0220
ARTV

Sai wani babban abin takaici ashe gwamnatin da ya ke so yake karewa itace zata tsigeshi daga mukaminsa, duk irin gwagwarmayar da yayi.

Sai dai mukamin da aka baiwa El Mustapha duk da cewa shima an hada Shi fada da abokan Sana’ar sa, a maimakon a lalubo hanyar taimaka musu, sai aka mayar da hankali Kan maganar haraji ta hanyar soke lasisin su

Iya bincike da muka gabatar wasu Abubuwan Da ake kullawa mai girma Gwamna ba shi da masaniya kan wannan kulle Kullen da ake yiwa wannan masana’anta duba da sanin muhimmancin yan masana antar da kuma irin gudunmawar da suka ba shi! Don haka muke amfani da wannan kafar domin sanar da gwamna irin wainar da ake toyawa

Sakon Yan Gwagwarmayar Kannywood masoyan KWANKWASIYYA

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *